Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga Zanga Biyu Sun Mutum a Haiti


Yanzu haka yan kasar Haiti sun bukaci shugaban kasar da ya sauka daga karagar mulki, saboda zarge zargen ci hanci da rashawa da ake zargin ya yiwa gwamantin katutu.

Harbe harben bindiga ya janyo tarwatsewar mutane a kan titinan da ke tsakiyar birnin Port-au-Prince a jiya Lahadi, inda har aka samu asarar rayuka biyu yayin da dubban ‘yan kasar Haiti suka yi zanga zanga kan matsalar cin hanci da ta yi katutu a gwanmnati.

Masu zanga zangar sun bukaci shugaba, Jovenel Moise, ya sauka kan zarge zargen almundahana da kuma kashe kudaden gwamanti ba bisa ka’ida ba.

Sun kuma sha al’washin ci gaba da zama a tituna har sai bukatunsu sun biya. Masu zanga zangar sun samu damar zuwa har kusa da gidan Shugaba Moise inda suke da tazarar mita 50 da gidansa na kansa da ke wata unguwa a wajen babban birnin kasar.

Sai dai ‘yan sanda sun dakatar da su daga sake matsawa da kuma tura karin wasu jami’an a gaban gidan shugaban kasar.

Wani hoton bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta ya nuna ‘yan sandan kwantar da tarzoma suna jefa duwatsu akan wani mutum wanda ake tunanin ya mutu, a lokacin da suke kokarin kewaye gidan shugaban kasar domin tabbatar da tsaro.

Sai dai rundunar ‘yan sandan kasar, ta ayyana bidiyon a matsayin “abin kunya” a wani sako da suka wallafa a shafinta na Twitter, inda ta ce “wannan ba ya daya daga cikin ayyukan da doka ta ba mu dama mu yi.”

Ta kuma kara da cewa, tuni an kaddamar da bincike kan wannan lamari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG