Mutane 38 aka hallaka, aka raunana wasu fiyeda 50 a cikin wata mummunar tarzomar da ta barke ranar Larabar shekaranjiya a Junhuriyar Afrika ta Tsakiya.
WASHINGTON, DC —
Ance tashin hankalin ya samo asali ne daga lokacinda mayakan ‘yantawayen Seleka suka abkawa garin Kanga-Bandoro inda sojan kiyaye sulhu na M-D-D suka tinkare su, har suka kashe 12 daga cikin ‘yantawayen.
Sai dai kuma cikin wadanda suka rasa rayukkan nasu akwai harda fararen hula 9.
Ana jin wannan farmakin kamar ramuwar gayya ce su mayakan Seleka din suka kai don rama kisan gillar da aka yi wa wani dan’uwansu, a cewar rundunar kiyaye sulhun MDD din.