Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Tsaro da Kwamandojin Rundunar Sojojin Hadin Gwuiwar Kasashen Yankin Tafkin Chadi Sunyi Taro A Nijar


Kwamandojin dakarun hadin gwuiwar kasashen yankin tafkin Chadi tare da ministan tsaron Nijar
Kwamandojin dakarun hadin gwuiwar kasashen yankin tafkin Chadi tare da ministan tsaron Nijar

Hausawa sun ce waiwaye adon tafiya shi ne taron da ministocin tsaro da kwamandojin dakarun kasashen yankin tafkin Chadi suka yi a Nijar inda suka yi nazari akan nasarorinsu da sauran kalubale da suke fuskanta

Waiwaye akan irin ayyukan da sojojin hadin gwuiwar kasashen tafkin Chadi da suka hada da Najeriya, Nijar, Kamaru, Chad da kuma Benin shi ne makasudin haduwarsu a taronsu a Jamhuriyar Nijar.

Suna nazari ne akan ainihin halin da yankin yake ciki a yau, yankin dake fama da hare-haren Boko Haram. Taron ya zo ne bayan zartas da matakan da suka shimfida a wani taron da suka yi a watanni hudun da suka gabata a kasar Chadi..

Hashimi Masa'udu Ministan Tsaron Nijar
Hashimi Masa'udu Ministan Tsaron Nijar

Hashimi Masa'udu ministan tsaron Nijar yace bayan taron da suka yi a babban birnin Chadi garuruwa da yawa da suke hannun 'yan Boko Haram a Najeriya duk an kwatosu. A yankin Diffa ma dake Nijar din sun yi yaki kuma yanzu ana samun sauki. Sun karkashe 'yan Boko Haram kuma yanzu basu da karfi kamar da.

Duk da nasarorin da suka samu akwai wani kalubale na daban wanda yake da alaka da nakiyoyi da 'yan ta'adan suka binne a wurare daban daban. Sanusi Imrana Abdullahi wanda injiniya ne kuma shi ne sakataren kasashen yace tabbatar da lallai 'yan Boko Haram sun binne nakiyoyi. Yanzu kokarin da su keyi shi ne na tonowa da kunce nakiyoyin.

Can baya kungiyar kasashen na yankin tafkin Chadi ta koka da rashin kudi saboda wadanda suka yi alkawarin taimakawa da kudi basu cika alkawarinsu ba. Abun da suke anfani dashi shi ne kudin da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayar. Cikin dala dari da shugaban Najeriya yayi alkawari ya bada tamanin da takwas shaura goma sha biyu da suke kyautata zato zai biya da zara ya samu kudi.

Kasashen duniya da suka dinga yin alkawari basu tabuka ba ba baicin taimaon da ba na kudi ba da aka ce sun ba kasashen.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG