An kashe mutane 31 a wani hari da aka kai a jihar Borno

BORNO: Harin kunar bakin wake a Maiduguri

Hare Haren kunar bakin wake sun janyo mummunan asarar rayuka da kuma raunata mutane da dama yayinda ake shagulgulan Sallah a Najeriya

Hukumomi sunce hare haren kunar bakin wake sun kashe a kalla mutane talatin da daya a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Fashewar ta auku ne yau lahadi a garin Damboa. Babu kungiyar da ta dauki alhakin harin nan da nan.

Ana dorawa mayakan kungiyar Boko Haram alhakin hare haren bom da ake kaiwa a yankin a lokutan baya.

Ana dorawa kungiyar Boko Haram alhakin mutuwar kimanin mutane dubu ishirin tun daga lokacin da suka fara tada kayar baya a arewacin Najeriya a shekara ta dubu biyu da tara. Kungiyar mai kaifin kishin Islama tace tana so ta kafa shari’ar musulunci a arewacin kasar da galibi Musulmi ne.