Masu zanga-zanga akalla biyu ne aka kashe lokacin wata arangama tsakanin masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da ‘yan sandan Iran jiya Asabar.
Cikin wani hotan bidiyo da aka kafe a kafar sadarwa na ikirarin nuna masu zanga-zangar biyu bayan da jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma suka harbe su garin Dorud dake yammacin kasar, yayin da zanga-zangar ta koma tashin hankali.
Sashen Fasha na Muryar Amurka ya bayyana mutanen biyu da aka kashe da suna Hamzeh Lashni da Hossein Reshno. Wakilkin sashen Fasha yayi magana da iyalan wadanda aka kashen.
Haka kuma wani hotan bidiyo da aka kafe a kafar sadarwa, shima yayi ikirarin nuna masu zanga-zangar sun kaiwa gine-ginen gwamnati hari, kuma na nunaalamar sun shiga mummunar arangamar da aka yi da ‘yan sanda. Hotunan bidiyo da ba a tabbatar da sahihancinsu ba a yanar gizo, sun nuna yadda dubban mutane ke zanga-zanga a birane masu yawa a kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP ya fitar da rahotan cewa an katse layukan waya da kuma yanar gizo kafin tsakar daren jiya Asabar. Ta kuma rawaito kafar labaran Iran mai alaka da gwamnati cewa an hana ta yada labaran zanga-zangar kin jinin gwamnati.