WASHINGTON D.C. —
Akalla mutum biyar jami’an tsaron Iraqi suka harbe har lahira bayan da suka yi amfani da harsashen gaske akan masu zanga zanga a Bagadaza, a cewar ‘yan sanda da jami’an asibiti.
Jami'an tsaro sun yi harbe-harbe a kan masu zanga-zangar wadanda suka kusanci ofishin firaiminista da nisan mita 500 a jiya Litinin.
A baya, jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashen roba domin hana masu zanga-zangar da suka yi kokarin ketara shingayen da aka dasa tsakaninsu da ofishin firaiministan.
Akalla mutane 250 aka kashe tun da aka fara zanga-zangar adawa da gwamnati a farkon watan Oktoba a kasar ta Iraqi.