Firaiministan Lebanon Sa’ad Hariri, ya yi murabus daga mukaminsa a jiya Talata, bayan kwanaki 13 da aka kwashe ana wata zanga zangar adawa da gwamnati, wacce kasar ba ta taba ganin irinta ba, inda jama’a suke neman a yi sauye-sauye a fannonin siyasar kasar da na tattalin arziki.
“Na yi iya bakin kokarina na ga cewa an samu mafita, a saurari korafe-korafen jama’a, a kare tattalin arzikin kasa da tabbatar da tsaro, amma bari na fada muku gaskiya, abin ya cutura.” Inji Hariri.
Hariri wanda ya yi wannan jawabi kai-tsaye ta kafar talbijin ga daukacin al’umar kasar, ya mikawa shugaba Michel Aoun takardar murabus dinsa.
Masu zanga zangar dai na nema ne a yi sauye-sauye a fannin tattalin arzikin kasar tare da yin garanbawul a mukaman da ‘yan siyasa ke rike da su, wadanda ake zargin suna barnata arzikin kasar kuma ba su ma cancanta su rike su ba.