An Kashe Masu Zanga Zanga A Kusa Da Hukumar Zabe A Afghanistan

Afghanistan

An kashe akalla mutane biyu wasu hudu kuma sun jikata bayan wata fashewa da wani dan kunar bakin wake ya tayar a kusa da ofishin hukumar zabe a birnin Jalalabad dake arewa maso gabashin Afghanistan, a cewar jami’ai a yau sabar.

Jamia’an sun ce fashewar ta faru ne yayin da maharin ya tinkaro tarin jama’a da suke zanga zanga a kusa da ofishin hukumar zabe. Suna zanga zangar ne domin nuna adawa ga shawarar dakatar da wani dan takara da ake zarginsa da alaka da kungiyoyin mayakan sa kai.

Darektan kiwon lafiya na gundumar Nangarhar, Najib Kamawal da Attahulla Khogyani mai Magana da yawun gwamnan Nangarhar, sun tabbatar da an kashe akalla mutane biyu.

Khogyani yace mun fadawa masu zanga zangar, da su fasa taronsu, saboda 'yan bindigar zasu iya aunasu, amma sai suka yi watsi da sakon jami’an tsaron mu.

Khogyani ya fadawa kampanin dillancin labarai na Associated Press cewa akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutun ya karu.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin na safiyar yau Asabar, amma dai kungiyoyi masu alaka da IS da Taliban suna gudanar da ayyukansu a yankin arewa maso gabashin kasar.