A farkon watan nan Amurka ta ayyana cewa za ta kara kudaden haraji akan kayayyakin China da ake shiga da su Amurka da kashi 25, wadanda kudinsu ya kai dala biliyan 16, dadi akan harajin da ta saka akan kayayyakin Chinan da kudinsu ya kai dala biliyan 34, a watan Yuli.
Ita ma China ta bi sahun Amurkan wajen mayar da martani da makamacin kudaden harajin da aka saka mata.
A jiya Alhamis, ma’aikatar cinikayya ta China, ta fitar da wata sanarwa, inda ta soki sabbin kudaden harajin, matakin da ta ce ya sabawa ka’idojin kungiyar cinikayya ta Duniya - WTO, tana mai cewa, za ta shigar da koke kan matakin da Amurka ta dauka a gaban kungiyar.
Sabbin kudaden harajin da Amurka da Chinan suka sakawa junansu, na zuwa ne bayan da aka yi zaman kwana guda, daga cikin kwanaki biyu da suka shirya za su yi a Washington, domin neman maslahar wannan takaddama ta cinikayya.
Facebook Forum