Wadanda suka tsira daga munanan matakan sojin a watan Agustan shekarar 2017 sun shaidawa masu aikin agaji a Bangladesh irin ta’asar da aka musu, wanda suka kunshi yi wa ‘yan uwansu fyade da kashe su a gaban su da kuma kone kauyakun su duk dan kar su sake komawa wajen.
Mutanen Rohingya dubu dari biyar ne suka yi gudun hijira zuwa Bangladesh a watan farko kana kimanin dubu dari biyu suka biyo baya a sauran wataninn. Yanzu haka suna zaune Cox Bazar, sansanin ‘yan gudun hijirar da ya fi kowanne girma da yawan mutane a fadin duniya.
“ Wannan wani abu ne da zamu bayyana a matsayin kisan kiyashi da nufin shafe wata kabila” a cewar Adama Deing, babban mai bada shawara a majalisar dinkin duniya kan hana kisan gilla, Kalaman nasa sun yi daidai da abinda shugabansa , babban sakataren MDD Antonio Guterres da kuma babban kwamishinan kwato ‘yancin bi’adama Zeid Ra’ad Al Hussein suka fada tun farko.
Facebook Forum