Majalisar Dinkin Duniya, ta ce an kashe dakarunta da ke wanzar da zaman lafiya a jiya Laraba, yayin da motarsu ta taka nakiya a tsakiyar kasar Mali.
Rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar ta Mali da aka fi sani da MINUSMA, ta ce dakarun na tafiya ne a tsakanin Boni da Dountza a yankin da ake kira Mpoti.
Baya ga wadanda suka mutu, wasu dakarun hudu sun samu munanan raunuka a cewar rundunar.
A ranar Talatar da ta gabata aka kashe wasu dakarun Mali shida a wannan yanki, a wani lamari mai kama da wannan.
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric, ya ce, Sakatare Janar, Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da wadannan hare-hare da aka kai akan dakarun.
Ya kuma ce, wannan hari, wanda ya kwatanta a matsayin na “ragwanci” ba zai kashe wa rundunar ta MINUSMA kwarin gwiwa ba, a yunkurin da ta ke yi na ganin mutanen Mali sun samu zaman lafiyan da suke muradi.
A shekarar 2013 aka tura dakarun na Majalisar Dinkin Duniya su 11,000 zuwa Mali, domin yakar masu tsatsauran kishin addini da kuma tabbatar da doka da oda.