Mataimakin kakakin Majalisar Dokokin jihar Filato, Yusuf Adamu Gagdi, yace sun gano kurakurai masu yawa a kundin dokar da ta ba damar gudanar da zaben kananan hukumomi da gwamnatin da ta gabata ta aiwatar.
Yace hakki ne a dokar Najeriya, Majalisar jiha ce keda hurumin yin dokoki a kananan hukumomi, hakan yasa suka dauki dokoki biyu da ake aiki da su domin yi musu kwaskwarima da kuma mayar da su a matsayin doka ‘daya tak.
Haka kuma ‘yan Majalisar zasu ‘dauki dokar da gwamnan jihar ya aika musu domin yi mata kwaskwarima, domin ganin anyi doka a hukumar zabe wadda ita kanta hukumar zaben bata da hurumin yin zaben da jam’a ba zasu amince da shi ba, kuma dokar da shi kansa gwamna bashi da hurumin fitowa yace an rusa zabe domin tabbaar da ganin abin da mutane suka zaba shine ya kasance.
To sai dai jama’ar jihar da dama sun nuna rashin gamsuwarsu da dalilan da Majalisar Dokokin ta bayar. Kamar yadda Madam Jummai Madaki, tace “An kara lokaci ne na bata lokaci” domin yin hakan na zaman tamkar an mayar da siyasar jihar baya ne.
‘Kusa a jam’iyyar APC reshen jihar Filato, Alhaji Jamilu Baba, na kira ne ga gwamnan jihar da ya tabbatar an gudanar da zaben, kasancewar ‘kin yin zaben kananan hukumomi illa ce ga dimokaradiyya.
Domin karin bayani ga rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5