An kara kudin wutar lantarki har da kashi 320 a Zimbabwe, yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsalar komadar tattalin arziki, wanda ba ta taba gani ba cikin sama da shekara goma.
Hukumar kula da makamashi a kasar da ake kira ZERA a takaice, ta ce ta yi na’am da matakin da kamfanin samar da wutar lantarkin ya dauka na karin kudi.
Yanzu jama’ar kasar za su rika biyan Centi 162 a maimakon Centi 38 a kowanne ma’aunin wuta na kilowatt da za su sha.
Wannan matakin karin kudin, shi ne na biyu da hukumomin kasar suka dauka cikin watanni uku.
A watan Agustan da ya gabata, an kara kudin wutar da kashi 400, inda gwamnati ta ce, matakin da ta ce ya zama dole ta dauka, domin ana bukatar kudaden da za a rika kula da kayayyakin aiki a kuma rika sayen man da za a sakawa injina domin su yi aiki.