Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Zaben Majalisar Dokokin Kasar Tunisiya


Yayin da aka rufe runfunan zaben majalisar dokokin kasar Tunisiya jiya Lahadi, jam'iyyar Ennahda mai sassaucin ra'ayin Islama ta doshi yin nasara.

Sakamakon binciken jin yadda jama'a su ka kada kuri'unsu, ya nuna jam’iyyar Ennahda na iya lashe kujeru wajen 40 daga cikin jimlar kujeru 217, yayin da jam’iyyar Heart of Tunisia, ta su hamshakin mai kafofin labaran nan, Nabil Karoui kuma na iya cin kurjeru 30 zuwa 35.

Sai dai babu wata jam’iyya da ake tunanin za ta iya samun cikakken rinjaye, wanda hakan ya na nufin duk wacce ta yi nasara dole ne ta kafa gwamnatin rikon kwarya.

Zaben, wanda shi ne na biyu tun da aka hanbarar da Shugaba mai fada aji Zine El Abidine Ben Ali a lokacin boren juyin juya hali na kasashen Larabawa a shekarar 2011, ana masa ganin zakaran sanin dafin makomar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da za a yi ranar 13 ga watan Oktoba.

Duka jam’iyyun biyu sun kira taron manema labarai jiya Lahadi, inda su ka yi ikirarin yin nasara. Ana kyautata zaton za a bayyana sakamakon zaben a yau Litinin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG