taron wanda aka gudanar a kasar Indonesia, ya samu wakilcin jihohin Naija da Sokoto. Wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Babangida jibrin, ya zanta da wakilan jihar Naija a wajen taron da aka kammala inda ya nemi jin ta bakinsu akan yadda za a gudanar da wannan shiri ganin yadda Najeriya, kasa ce bata al’ummar musulmai zalla ba.
A tattaunawarsu Imam Umar Abdullahi, darakta mai kula da addinin Islama, a jihar Naija, ya bayyana cewa ba lallai sai kasa ta kasance mai bin tsarin addinin musulunci ba, indai akwai musulmin da zasu ci moriyar shirin.
Imam Abdullahi, ya kara da cewa babu wani shiri da gwamnati zata kaddamar domin yaye talauci tsakanin al’umma kamar zakka, domin ita zakka wajibi ce. Daga karshe ya yi kira ga gwamanati ta gwada amfani da wannan tsari na amfani da zakka wajen rage radadin talauci a tsakanin al’umma.
Alhaji Tanko Baba Ahmad, Magatakardan Bargu, mai ba gwamna shawara akan harkokin Islama, kuma daya daga cikin mahalarta wannan taro ya bayyana cewa Zakka tana taimakawa tattalin arzikin kasa musamman idan an sarrafa ta yadda ya kamata.
Samun shugaba wanda yake adali, mai sanin yakamata, yana taimakawa jama’a samun karfin gwiwar fitar da zakka domin akasin hakan shike sa jama’a da dama samun rauni wajan fitar da zakka kamar yadda ya kamata.
Ga rahoton Babangida Jibrin Daga Legas.
Your browser doesn’t support HTML5