Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Bashi Da Hurumin Korar Fulani Daga Jihar


Shanun Fulani Makiyaya
Shanun Fulani Makiyaya

Matakin da Gwamnan jihar Benue, Mr Samuel Ortom ya dauka na korar Fulani makiyaya daga jihar, zai cigaba da jawo cece-kuce a tsakanin kungiyoyin Fulani makiyaya, da 'yan rajin kare hakkin bani Adama da kuma gwamnatin jihar a bangare guda.

A ranar alhamis data gabata gwamnan jihar Samuel Ortom ya sake nanata cewa sun dauki wannan mataki ne don kare rayukan al’umman jihar bisa abun da ya kira hare-haren da Fulani makiyaya ke kaiwa a wasu yankunan jihar.

Kungiyoyin Fulani makiyaya a Najeriya sun maida martani da cewa ba zasu amince da wannan matakin da gwamnati ta dauka ba, yayin da masana ke gabin akwai bukatar kai zuciya nesa.

Alh.Alkali Bello Wazirin Madagali shike jagorantar kungiyar makiyaya ta Weti-Weli Cattle rearers, a Najeriya, yace sun yi tir da kalaman da gwamnan jihar ke yi cikin kwanakin nan.

Yana mai cewa zasu yanzu haka suna shirin gudanar da wannan gangami na masamman a Abuja don mika kukansu ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Shima shugaban kungiyar Tabital –Pulaku Njode-jam ta Najeriya, Alh. Abdu Bali ya shawarci gwamnatin jihar Benue da a koma a hau teburin sulhu domin gano bakin zaren magance irin fitittunun dake aukuwa a tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu kabilun jihar ta Benue.

Wani lauya mai zaman kasan Barrister. Sunday Joshua Wigra ya ce akwai bukatar karatun ta natsu a wannan lamarin domin a cewarsa Gwamnan bashi da hurumin yace wasu mutane su bar masa kasa sai dai idan mutun yayi laifi ayi bincike sanan a hukunta shi.

Ba tun yau bane dai ake samun rashin jituwa a tsakanin makiyaya Fulani da kuma gwamnatin jihar Benue, da a baya ya kai ga makiyayan suka kauracewa jihar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG