Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mayakan Boko Haram Sun Mika Wuya Ga Sojojin Najeriya


Boko Haram
Boko Haram

Wasu mayakan Boko Haram guda tara sun ajiye makamansu sun kuma mika wuya ga sojojin Najeriya a ‘kauyen Tambashe dake karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno.

A cewar kakakin sojojin Najeriya janal Sani Usman Kuka Sheka, mayakan na Boko Haram sun mika wuya ne ga sojojin Najeiriya dake yin sintiri a yankin, inda suka ce sun gaji da wannan ta’addanci da suke yi saboda baya tsinana musu komai.

Yanzu haka dai ana nan ana ci gaba da tantance su, sai dai saboda lamarin tsaro kakakin bai sanar da inda aka ajiye mutanen ba.

Kuka Sheka, ya yi kira ga sauran mayakan Boko Haram da cewa wannan akidar da suke bi ta ta’addanci ba akida bace kuma ta yi wa duk wani tanadi da addinin musulunci yayi kara tsaye.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:48 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG