Matan kungiyar zumuntar ECWA ta kasa da kasa sun kammala taronsu tare da gargadin junansu yadda zasu sarrafa iyalansu ta hanyar koyarwar Ubangiji don dakile matsalolin tsaro da ake fuskanta a sassa daban-daban na duniya.
WASHINGTON D.C. —
Taken makon na wannan shekar shine yadda mata zasu kasance da farin ciki, duk da matsalolin da ake fuskanta a wannan karni na ishirin da daya.
Madam Tabitha Guruza, ta ce sun koyi yadda zasu sarrafa gidansu, su taimaka wa mazajensu, su kuma kawo karshen shaye-shaye da matasa ke yi dake sasu fadawa cikin rikici.
Ita ma Madam Hannatu Jugo ta ce addinin kirista yana koyar da kauna ne ga kowa.
Madam Esther Hayap ta ce sun koya wa mata suyi bishara su kuma koya wa ‘ya’yansu kyawawan halaye.
A cikin mako guda da matan suka yi ibada, sun sami koyarwa a littafi mai tsarki sun kuma yi adduo’i don kasa ta zauna lafiya.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5