Hedkwatar Sojojin Najeriya tace an cafke wasu jami’anta da makamai zasu kai inda ba’a sani ba. Kakakin rudunar Sojan Najeriya, Kanal Sani Usman Kuka Sheka, yace duk da kokarin da rundunar keyi amma sai kasha wasu bata gari a cikinsu na faman maida hannun agogo baya.
Yace “ Ana samun bata gari daga coikin Sojojin mu domin ranar lahadinnan data wuce biyu daga cikin su an kama su a tashar Mota ta Yola, da wasu makamai da albarusai, wanda bai kamata ba, suna neman su kais u wani guri, wadanna Sojoji sune Eric Onwokore da Marcauley Fortune, abubuwan da aka same su dasu sun hada da Gurneti, albarusai fiye da 2000, da wasu albarusai na masamman 50, akwai albarusai na bindigogi masu sarrafa kansu.”
Ya kara da cewa wasu marasa kishi daga cikin ‘yan kasuwa a jihohin Borno da Yobe na amfani da kasuwani Kauye wajen tallafawa ‘yan Boko Haram, akwai wasu mutane da basu da Imani suna amfani da wata dama ta bude kasuwani da akayi a jihohin Bornoda Yobe, suna amfani da wannan harka ta kasuwanci suna hada baki da ‘yan ta’adda na Boko Haram, suna kai masu abubuwa don haka muke so mu shedawea duniya cewa zamu dauki wasu tsauraran matakai kamar rufe wadanna kasuwani, an baiwa kwamandoji da suke bakin daga da su aiwatar da haka.
Your browser doesn’t support HTML5