Da yake bayyanawa Muryar Amurka yadda lamarin ya faru, babban limamin masallacin Orlu, mallam Abubakar Musa, ya ce mutanen biyu sun je bakin masallaci akan babur ganin yawan jama’ar dake gurin yasa suka hau babur dinsu suka tafi.
A kan hanyarsu ne jami’an ‘yan sanda suka tare su domin bincikarsu sai daya daga cikin mutanen biyu ya fadawa ‘yan sandan cewa shi jami’in soja ne, inda nan take suka nemi katin shaidar aiki, amma babu.
Lokacin da ‘yan sandan suka karbi jakar dake hannu guda daga cikin mutanen biyu, nan take suka gano cewa bam ne.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin kwamishinan ‘yan sandan jihar Mallam Dasuki Galadanci, ya ce yanzu haka sun mika bam din gas ashen dake warware bama-bamai domin gano abubuwan da aka hada bam da shi.
Haka kuma hukumar ‘yan sandan jihar Imo na gudanar da bincike domin gano daga inda aka hada bam din da kuma masu hannu a wannan lamarin.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Alphonsus Okoroigwe.
Your browser doesn’t support HTML5