An Kama Wasu Masu Zanga Zanga A Amurka

Tun bayan da wasu jami'an 'Yan sanda biyu farar fata suka harbe suka kashe bakar fata biyu makon jiya, ana ta zanga zanga a wurare daban daban a fadin kasar.

An kama masu zanga zanga masu yawa, a wuri guda inda lamarim yafi tsanani shine a birnin Baton Rouge Lousiana, inda aka kama Deray Mckesson, wani fitacce a kungiyar masu gwagwar mayar ganin an kawo sauyi a hukumomin 'Yansanda a Amurka, kungiyar da aka fi sani d a sunan Black Lives Matter a turance, wanda ke nufin rayukan bakar fata yana da tasiri.


Lamarin da ya janyo kwanton baunar da ta kai ga kisan 'Yan sanda biyar a birnin Dallas na jihar Texas, da jikkata wasu bakwai. Baturen 'Yan sandan birnin David ya gayawa tashar talabijin ta CNN jiya lahadi cewa lamarin da ya fi haka muni.


Shugaban 'Yan sandan yace maharin Micah Xavier Johnson dan shekaru 25 da haifuwa ya gayawa jami'an 'Yan sanda masu shiga tsakani cewa "yana son ya kashe fararen fata, musamman jami'an 'Yan sanda."


Jami'an tsaro sun gano kayan harhada bama-bamai da kasida a gidan Johnson ranar Jumma'a, lokacin da suka gudanar da bincike.


Shugaban 'Yan sandan Brown yace kayana hada bama-baman suna da yawan da zasu haddasa mummunar illa a duk fadin birnin dama Arewacin Texas baki daya inji Brown.


Ahalinda ake ciki kuma shugaban Amurka Barack Obama, yana kira ga Amurkawa su mutunta juna, kwanaki bayan da 'Yansanda suka harbe suka kashe wasu bakar fata biyu, da kuma harin kwanton baunar da ya halaka 'Yansanda biyar a birnin Dallas.


Shugaba Obama wanda yake ziyara a Turai, bayan ya halarci taron kungiyar tsaro ta NATO, zai katse ziyararsa da kwana daya. Ana sa ran ya dawo Washington jiya lahadi domin ya kai ziyara birnin Dallas cikin 'yan kwanaki masu zuwa.