Shugaban jam’iyyar Bill Shorten yace yana da yakinin Firaministan Malcolm Turnbull da gwamanatin hadakarsa sun lashe mafi yawan kujeru.
Wanda hakan zai basu damar ci gaba da kasancewa a karagar mulkin kasar. Don haka Bill yace ya kira Firaminista Turnbull ya taya si murna ta waya.
Turnbull yace shi da tawagar hadin gwiwarsa masu ra’ayin ‘yan mazan jiya za su ci gaba da wa’adin mulkin shekaru 3 a karo na biyu.
Sai dai har yanzu da ake ci gaba da kidaya kuri’un da aka kada, ba a tabbatar ko tawagar hadakar zasu sami isassun kujerun da zasu zama masu rinjaye a gwamnatin ba, ko kuma zasu gaza da har sai sun hada kai da ‘yan tsirari don kafa gwamnatin marasa rinjaye ba.
Jam’iyya sai ta akalla kujerun 76 daga kujeru 150 a Majalisa kan ta sami zama mai rinjaye. Zabe a Australia dole ne, shi yasa jama’ar kasar suka yi dafifin kada kuri’unsu a makon daya da ya wuce.