Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Zai Je Dallas Kan mutuwar Bakaken Fata 2 Da 'Yan Sanda 5


Obama
Obama

Shugaban Amurka na ta kokarin ba Amurkawa kwarin gwiwa game da kaduwar da suka yi na harbin wasu Amurkawa bakaken fata guda 2 da kuma kashe ‘yan sanda 5 da aka yi a Dallas.

Na kwanton baunar da wani bakar fata ya yiwa a lokacin zanga-zangar birnin Dallas na jihar Texas, inda ya yiwa ‘yan sanda dauki dai-daya ya kashe guda 5 tare da jikkata guda 7.

Obama wanda abin ya faru yana wajen taron rundunar tsaro ta NATO a birnin Warsaw, ya karkata akalar jawabinsa ne game da abinda ke faruwa a kasarsa a lokacin da yake taron manema labarai.

Ya kuma takaita tafiyarsa da ta Turai da kwana daya don komowa gida a jiha Lahadi da daddare don fuskantar yadda za’a shawo kan matsalar. Sannan ya bayyana cewa zai isa birnin Dallas a ‘yan tsakanin nan bisa gayyatar da Magajin Garin ya masa.

Game da faruwar wannan matsala, Shugaba Obama yace, ba zai daina jingina faruwan wadannan matsalolin da rashin yin takunkumi game da mallakar bindiga barkatai ba. Wanda yace yana taka rawa sosai wajen yin aika-aika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG