An Kama wani dan asalin kasar Libya a Jamus, wanda ake zargi da kitsa kai farmaki ofishin jakadancin Isra’ila a birnin Berlin sannan an alakanta shi da kungiyar IS wanda za a gabatar da shi a gaban kuliya yau Lahadi, a cewar mahukunta a Jamus.
Omar A., shine wanda aka bayyana a matsayin wanda ake zargin wanda aka kama da yammacin ranar asabar a gidan shi dake Bernau, a wajen babban birnin kasar ta Jamus, bisa bayanan ofishin mai shari’ar tarayya.
Ana zargin Omar da kitsa kai wani “mumunan hari da makamai”a ofishin jakadancin Isra’ila a Berlin. Daga cikin abubuwan da yayi na shirin kai harin, an zargi Omar A. da tuntubar wani dan kungiyar masu tsatsaurar ra'ayin Islama ta Islamic State, wato IS ta manhajar aike sakonni,” inji masu shari’ar, da suka bayyana shi da mai tallafawa manufofin kungiyar.
A wani sako da jakadan Isra'ila a Berlin ya wallafa a shafin sa na X, ya ce, “kin yahudawa da Musulmai suke yi, yanzu ya wuce batun kiyayya kawai. Yakan kai ga baiwa masu aikata ayyukan ta’addanci kwarin gwiwa a fadin duniya.”
Sannan ya kara da cewa, "Ofisoshin jakanacin Isra’ila suna fafatawa a fagen yaki a fannin difflomasiyya,” sakon da Ambasada Ron Prosor ya wallafa kenan.
Ministar cikin gidan Jamus Nancy Faeser, ta ce kare yahudawa da ofisoshin Isra’ila a Jamus, batu ne mai “matukar mahimmanci a gare mu.”