SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da hukumar da ke yaki da hada-hadar miyagun kwayoyi suka damke wani basarake wanda ke dillancin wiwi da kwayoyi a Jihar Sokoto, abin da ya sa masana ke ganin wata ishara ce ga mahukuntan kasar.
Batun sha ko hada-hadar miyagun kwayoyi ya jima yana ci wa 'yan Najeriya tuwo a kwarya duk da kokarin da mahukuntan ke yi na dakile matsalolin wanda ke da mummunar illa a cikin al'umma, musamman ga matasa.
Wannan karon wani basarake, jami'in da ke yaki da sha da safarar miyagun kwayoyin suka kama a Sokoto da hannu dumu-dumu ga dillancin kayan na maye.
Kwamandan hukumar a jihar, Adamu Muhammad Iro, ya ce sun share wata hudu suna kokarin kama basaraken amma sai yanzu ne suka samu nasara, dubunsa ta cika.
Wannan batun yana zuwa ne lokacin da 'yan kasa ke ci gaba da tsokaci tare da nuna yatsa ga hukuma akan yawaitar wadannan matsalolin a kasar.
Masana halayyar dan Adam na ganin wannan ba abin mamaki ba ne a samu shugaban jama'a da hannu ga aikata ba daidai ba, sai dai ya kamata ya kasance ishara wajen samar da shugabanni nan gaba, a cewar Farfesa Tukur Muhammad Baba.
Haka kuma jama'a na ganin su ma wadanda ke fafatukar dakile wannan safarar ya kamata a kara yawansu tare da karfafa musu gwiwa da samar da kayan aiki, kuma su kasance masu gaskiya, ta yadda za su iya kakkabe wannan muguwar safara a cikin al'umma.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5