Jami'an tsaron Nijar sunyi nasarar kama mutane 15 da kimanin kwaya miliyan biyu na Kiptagon wanda yan ta'adda da kuma yan boko haram ke amfani da ita.
Wannan ne karon farko da jami'an tsaro a Nijar su kayi nasarar kama irin wannan kwaya mai suna kiptagon wacce ake shigo da ita daga kasar Aljeriya.
Jami'an tsaro sun tabbatar da cewa kwaya ce da ake shirin sayar wa yan ta'adda ita.
A wannan shekarar kusan ba a wuce wata guda a kasar Nijar ba tare da jami’an tsaro na yan sanda dake yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a kasar sun yi nasarar kama wasu masu fataucin miyagun kwayoyi irin su tramadol, tabar wiwi da kuma uwa uba cocaine ko hodar iblis.
Kungiyoyin farar hula sun jinjinawa jami’an tsaro game da irin kokarin da suke yi ba dare ba rana wajen farautar masu safarar miyagun kwayoyi
Jihar Agadas dai ta zama wata hanyar da masu safarar miyagun kwayoyi kebi domin shigar da kwayoyin koma wuce dasu zuwa wasu kasashe kamar libiya da Aljeriya saboda haka jami’an tsaron sukayi kira ga al’umma da su basu gudun mawar da ta dace
Masu fataucin miyagun kwayoyi yanzu haka da dama ne dai suka riga suka shiga hannu wasunsu yan kasashe makwabta, wasu kuma yan kasar Nijar.
A saurari cikakken rahoton Hamid Mahmud:
Your browser doesn’t support HTML5