Wani alakalin kotun tarayya a Jihar Maryland ya ki ba da belin wani dogarin gabar ruwa mai suna Christopher Paul Hasson a jiya Alhamis wanda ake zargin ya tattara makamai don kaddamar da harin ta’addanci da kuma kashe mutane da yawa a cikin Amurka.
Alkali Charles Day ya bada umarnin ya ci gaba da zama a gida yari zuwa nan da sati biyu yayin da masu gabatar da kara su ke duba yiwuwar kara wasu cajin akan sa.
Yan sanda sun kama Hasson a makon daya gabata bisa zargin mu’amala damiyagun kwayoyi da makamai. Sannan sun gano shirinsa na kashe fararen hula wadanda basu-ji-ba basu gani ba da yawa a kasar, “a cewar wasu takardun karar da gwamnatin ta shigar.
Jami’an sun gano bidigogi goma sha biyar da kuma dubban harsasai a cikin gidansa da ke wajan a rukunin gidajan Washignton. Gwamnatin bata bayyana hakikanin abinda yasa take binciken Hasson tun da farko ba.