Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio ya ce an kama galibin jagororin da suka kai hare-hare kan manyan barikin soja da gidajen yari na kasar kuma komai ya koma daidai a fadin kasar bayan da aka sassauta dokar hana fita ta sa'o'i 24, shugaban ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi wa al'umar kasar a daren Lahadi.
Hare-haren da aka kai da sanyin safiyar Lahadi sun ba 'yan kasar da jami'an tsaro mamaki tare da janyo fargabar yiwuwar juyin mulki a yankin na yammacin Afrika mai fama da rikice-rikice.
Mazauna Freetown babban birnin kasar sun wayi gari da jin karar harbe-harben bindiga a lokacin da 'yan bindiga suka yi kokarin kutsawa cikin wata ma'ajiyar makamai da ke barikin soja mafi girma a kasar, a kusa da fadar shugaban kasa.
Maharan sun dauki lokaci mai tsawo suna musayar wuta da jami'an tsaro, sun kuma kai hari kan manyan gidajen yari, ciki har da gidan yarin da ke da fursunoni sama da 2,000.
Hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda fursunoni da dama suka yi ta kwarara zuwa kan tituna domin su tsere cikin sauri, a daidai lokacin da jami'an tsaro suka yi artabu da mahara a wajen birnin.
Hare-haren sun kara zafafa rikicin siyasa a yammaci da tsakiyar Afirka inda aka samu karuwar juyin mulki, yayin da sojoji suka kwace mulki har sau 8 a kasashen yankin tun daga shekarar 2020, ciki har da Nijar, Gabon a bana. Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, wacce Saliyo ke cikinta, ta bayyana hare-haren a matsayin wani shiri na "samun makamai da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da tsarin mulki" a kasar.
"Wadannan hare-haren wani yunkuri ne na kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin da muka yi aiki tukuru akai," in ji Bio, wanda sake zabensa don wa'adi na biyu da aka yi a watan Yuni ya janyo rikicin siyasa a kasar da ke kokarin murmurewa daga yakin basasa da ta fuskanta tsawon shekaru 11, da aka kawo karshensa fiye da shekaru ashirin da suka wuce.
"Ana ci gaba da ayyukan tsaro da bincike kuma za mu tabbatar da cewa wadanda ke da alhakin kai hare-haren za su fuskanci hukuncin da ya dace," in ji Bio.
Dokar hana fita daga karfe 9 na dare zuwa karfe 6 na safe za ta ci gaba da aiki har sai abin da hali yayi, a cewar ministan yada labaran kasar Chernor Bah.
"Yayin da muke karfafa 'yan kasar da su koma harkokinsu na yau da kullum, muna ci gaba da neman kowa ya kwantar da hankalinsa amma a sa ido, kuma idan an ga wani da ba a saba gani ba a sanar da ofishin 'yan sanda mafi kusa," in ji Bah.
~ AP