Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SALIYO: Mutane Uku Sun Mutu A Zanga Zangar Kin Jinin Gwamnati


Zanga zangar kin jinin gwamnati a Freetown
Zanga zangar kin jinin gwamnati a Freetown

Akalla jami’an ‘yan sanda shida da kuma farar hula goma sha uku ne suka mutu bayan an wuni ana zanga zangar kin jinin gwamnatita a Freetown babban birnin kasar Saliyo, kamar yadda wani ma’aikacin dakin ajiye gawarwaki na birnin ya bayyana jiya Laraba.

A baya dai gwamnatin Saliyo ta ce an samu asarar rayuka, sai dai bata bayyana adadin wadanda suka mutu ba, yayin da masu zanga zangar suka yi ta jifa da duwatsu da kona tayoyi a kan tituna saboda nuna takaicin tabarbarewar tattalin arziki da sauran batutuwa.

Kasar ta Yammacin Afirka, wacce ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da matsalar man fetur, ta sanya dokar hana fita a fadin kasar daga karfe 3 na yamma agogon kasar, a wani yunkuri na dakile tashin hankalin.

Zanga zangar kin jinin gwamnati a Freetown
Zanga zangar kin jinin gwamnati a Freetown

Shugaban kasar Julius Maada Bio ya wallafa a shafinsa na twitter cewa “A matsayinmu na gwamnati, muna da alhakin da ya rataya a kan mu na kare duk wani dan kasar Saliyo. Abin da ya faru a yau abin takaici ne kuma za’a yi bincike sosai.

Baya ga gawarwakin ukun da ke dakin ajiyar gawarwaki, wani dan jarida na kamafanin dillacin labarai na Reuters ya ga gawar wani farar hula a kan titi a gabashin Freetown.

XS
SM
MD
LG