An Kai wa Tiwa Savage Hari A Gidanta

Tiwa Savage (Hoto: Shafin Instagram na Tiwa savage)

“An kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin, kuma ana tsare da su a ofishin ‘yan sanda na Alagbon da ke Ikoyi.” Sanarwa wacce kamfaninta na Everything Savage ya fitar ta ce.

Wasu mutane da ba a bayyana su wane ne ba, sun kai hari gidan mawakiyar Afrobeat a Najeriya Tiwa Savage.

Lamarin ya faru ne a gidanta da ke Legas kamar yadda ta tabbatar a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Instagram a ranar Juma’a.

“Bayan rahotanni da suka bayyanaa a kafafen sada zumunta, muna masu tabbatar muku da cewa a ranar 13 ga watan Afrilun 2023, an yi wa matakan tsaro kutse a gidan mawakiya Tiwa Savage.

“An kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin, kuma ana tsare da su a ofishin ‘yan sanda na Alagbon da ke Ikoyi.” Sanarwa wacce kamfaninta na Everything Savage ya fitar ta ce.

Sanarwar dai ba ta ambaci wane irin hari aka kai gidan mawakiyar ba, amma tun gabanin fitowar sanarwar, wata ‘yar jarida mai zamanta da ake kira Kemi Olunloyo, ta bayyana cewa wasu ne suka yi yunkurin yin garkuwa da Tiwa.

“Tiwa da iyalanta suna cikin koshin lafiya.” Sanarwa ta kara da cewa.