An kai Tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir wani asibiti a arewacin kasar, wanda ya shafe shekaru 30 yana mulki kafin a hambarar da shi a wani boren jama’a,.
Bayan hambarar da shi, shugabannin sojojin kasar sun daure shi a gidan yari.
Lauyansa ya fada a ranar Laraba cewa an dauke al-Bashir mai shekaru 80 da haihuwa daga wani sansanin soji da ke wajen babban birnin kasar Sudan, Khartoum, a ranar Talata.
Lauyan ya kara da cewa lafiyar al-Bashir ta tabarbare a baya bayan nan, amma yanayin bai yi tsananta ba.
Haka kuma tsohon ministan tsaron Sudan Abdel-Rahim Muhammad Husseien ya koma arewacin kasar.
An kama shi ne jim kadan bayan hambarar da al-Bashir a shekara ta 2019.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dai tana neman mutanen biyu kan tuhumar laifukan yaki da kisan kare dangi.