Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakin Sudan Ya Haifar Da Matsananciyar Yunwa A Yankin Darfur

FILE - Residents wait to collect food in containers from a soup kitchen in Omdurman, Sudan, March 11, 2024. Nearly five million people in the country are close to famine as Sudan's civil war passes the one-year mark.

A cewar rahoton, an yi hasashen za'a fuskanci bala'in yunwa a karon farko a tarihin binciken shirin da ake kira IPC a Sudan.

Wani rahoto da hukumar sa ido kan karancin abinci da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a jiya Alhamis, ya nuna cewa yakin da aka shafe sama da shekara guda ana yi a Sudan ya jefa wasu sassan arewacin Darfur cikin kangin yunwa, ciki har da sansanin ‘yan gudun hijira, inda aka tsugunnar da mutane sama da rabin miliyan.

A cewar rahoton, an yi hasashen za'a fuskanci bala'in yunwa a karon farko a tarihin binciken shirin da ake kira IPC a Sudan.

An kuma ayyana yankuna 14 a matsayin masu fuskantar barazanar bala’in yunwa a cikin watanni masu zuwa, kamar yadda Kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric ya shaidawa manema labarai, game da mizanin IPC, shirin da ke sa ido kan karancin abinci na duniya.

Mizanin tsarin na IPC bai ayyana bala’in yunwa ba, amma ya ba da hujjojin da za'a ayyana bala’in yunwa a hukumance.

Sudan Hunger
Sudan Hunger

Tsarin na IPC ya ce matsalar yunwa ta fi kamari a arewacin Darfur, ciki har da sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam, wanda ke tazarar kilomita 12 kudu da El Fasher babban birnin yankin, kuma ta yiwuwa yanayin ya tsananta har zuwa karshen watan Oktoba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG