Kawo yanzu dai mutane uku ne aka tabbatar sun hallaka biyo bayan harin kunar bakin waken da aka kan sansanin ‘yan gudun hijira dake Malkohi a Yola fadar jihar Adamawan, wannan mako yazo ne kasa da awowi ashirin da hudu bayan da aka kawo wasu ‘yan gudun hijira daga Madagali da ma wasu ‘kauyuka dake makwabtaka da dajin Sambisa.
Babban jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta najeriya NEMA, Alhaji Sa’du Bello dake kula da sansanin na ‘yan gudun hijira dake jihar Adamawan ya bayyana yadda lamarin ya faru inda yace, “da safan nan karfe goma sha daya saura minti goma ne muka sami rahoton cewa wani abu ya fashe a sansanin na Malkohi, mun kuma garzayo domin ganin abinda ya faru.” Ya dai cigaba da bayyana cewa mutane uku Allah yayi musu rasuwa, yawancinsu kananan ‘yan mata ne da kuma mutanen da suka ji ciwo guda tara suna asibiti a halin yanzu.
Kawo yanzu jami’an agaji na NEMA suka kwashe gawarwakin mutanen da suka rasa rayukansu dama wadanda suka raunata zuwa asibiti. Har yanzu dai ba wani ko wata kungiyar da ta fito ta dauki alhakin kai wannan harin, yayin da jama’a a bangare guda ke fata Allah ya kawo karshen wannan matsala.
Your browser doesn’t support HTML5