Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Tace Tsauraran Dokoki Ne Zasu Magance Cin Hanci da Rashawa


Tutar kungiyar kwadagon Najeriya
Tutar kungiyar kwadagon Najeriya

A firar da kungiyar kwadago tayi da Muryar Amurka ta nemi gwamnatin tarayya ta kafa tsauraran dokoki tare da aiwatar dasu ta yin anfani da kotuna na musamman a matsayin hanyar da za'a yaki cin hanci da rashawa a Najeriya

Daya daga cikin shugabannin kungiyar kwadagon Najeriya Tura Khalil ya yi fira da wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya inda ya bayyana matsayin kungiyar akan yaki da cin hanci da rashawa.

Kungiyar dai ta shiga yin zanga zangar goyon bayan shugaba Buhari saboda yakin da ya shiga yi da cin hanci da rashawa tun lokacin da ya hau kujerar mulki.

A gangamin farko da shugabannin suka yi sun mika sakonsu ga wasu mahunkuntar kasar. Sun fara da hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC kafin su wuce majalisar dokokin kasa. Sai kuma ofishin sakataren gwamnatin tarayya inda nan ma suka mika wasikarsu.

Kungiyar tace yadda cin hanci da rashawa ya yiwa kasar katutu sai an kafa tsauraran dokoki kafin a shawo kansa. Akan haka kungiyar ta kira majalisar tarayya ta kafa tsauraran dokoki tare da kafa kotuna na musamman da zasu dinga yin shari'a akan cin hanci da rashawa kawai.

Abubuwan da suka faru da ko kuma suke faruwa yanzu su suka karfafa cin hanci da rashawa. Kungiyar tace a kasar ne wani ya handame biliyoyin nera na kudin fansho amma aka yi masa hukuncin daurin shekara biyu a gidan kaso ko kuma ya biya tarar nera 750,000. Hukuncin ya nuna kamar babu dokoki da zasu iya yakar cin hanci da rashawa ne.

Kungiyar ta kara kira a aiwatar da bincike har zuwa kananan hukumomi tare da binciken asusun hadin gwiwa na kananan hukumomin da jihohi da tace shi ne mahaifar cin hanci da rashawa.

Wajibi ne bincike ya hada da tsoffin kararraki na cin hanci da rashawa da aka yiwa rufa rufa. Kamata ya yi a bisu saboda a warwaresu.

Shugaban kungiyar Tura Khalil yace wajibi ne a kafa kotuna na musamman kamar yadda ake kafa kotunan zabe kana a duba dokokin da aka kafa hukumomi kamar EFCC domin su yi aikinsu yadda ya kamata. Sabanin haka kungiyar kwadago zata cigaba da yin zanga zanga musamman idan ta ji wani alkali ya hana binciken cin hanci da rashawa ko wani azzalumin gwamnati kamar yadda ya faru a baya..Kwana kwanan nan wasu tsoffin gwamnoni suka sheka kotu suka hana binciken da ake yi masu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

XS
SM
MD
LG