An Kai Hari Sansanin Horar Da Sojojin Mali

Mali

Babban hafsan sojin kasar Oumar Diarra ya ce  sojoji sun yi nasarar kashe maharan, amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Jami’ai sun ce hakan ya haifar da kazamin fadan bindiga da kuma rufe filin jirgin sama da ke kusa na wucin gadi kafin sojoji su samu nasarar fatattakar maharan.

Kawo yanzu dai ba’a bayar da cikakken bayani kan asarar rayuka ba. Mayakan sun yi kokarin kutsawa cikin makarantar Jandarma Faladie da ke birnin Bamako, lamarin da ya sa sojojin gwamnati daukar mataki nan take.

Babban hafsan sojin kasar Oumar Diarra ya ce sojoji sun yi nasarar kashe maharan, amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Wani jami’in tsaro ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na AP cewa harin ya haddasa “asara rayuka” da kuma “asarar dukiya” kuma an kama akalla mutum 15 da ake zargi suna da hannu a harin.