An Kai Hari Gidan Kakakin Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijar

Gidan Kakakin majalisar dokokin Nijar da aka kai hari

Gidan Kakakin majalisar dokokin Nijar da aka kai hari

Wannan shi ne karo na biyu da ake  kai hari a gidan shugaban jam’iyar MNSD Seini Oumarou a kasa da shekara daya.

A Jamhuriyar Nijar wasu ‘yan bindiga sun kai hari a gidan kakakin Majalisar Dokokin kasar Alhaji Seini Oumarou dake birnin Yamai inda suka hallaka jami’in tsaro daya suka jikkata wani daban, kafin su arce.

Tuni aka kaddamar a bincike don tantance dalilin kai wannan hari.

Maharan wadanda su biyu ne suka je gidan akan babur daya sun fara ne da bude wuta akan jami’an tsaron dake kofar gidan shugaban kakakin majalisar dokokin dake unguwar Koubia ta birnin Yamai kamar yadda mai magana da yawun kakakin majalisar Ousseini Salatou ya tabbatarwa da manema labarai.

Ya ce “jiya wajejen karfe 1 na dare wasu ‘yan bindiga dake kan babur sun kai farmaki a gidan Seini Oumarou. Kuma isowarsu ke da wuya suka bude wuta kan jami’in tsaron dake sintiri a kewayen gidan wanda a take ya rasu sannan suka kewaye ta bangaren babbar kofar gidan nan ma suka harbi jami’an tsaron dake wurin, harbi 4 suka yi masa amma kawo wannan lokaci da nake magana da ku muna yi wa Allah godiya bai rasu ba yana can asibiti kwance.” In ji Salatou.

Ya kara da cewa, daga bisani maharan sun yi kokarin arcewa da motar jami’an tsaro Toyota Pick up amma ba su yi nasara ba.

Ya kara da cewa ba wanda ya san masababin kai wannan hari saboda bincike ne kawai zai iya bada damar sanin su waye ke da hannu kuma mene ne dalilan kai harin.

Faruwar wannan al’amari ya sa wasu mazaunan birnin Yamai soma jan hankulan hukumomi da al’uma baki daya akan batun tsaro a birnin

Wannan shi ne karo na biyu da ake kai hari a gidan shugaban jam’iyar MNSD Seini Oumarou a kasa da shekara daya kuma wani harin da aka kai a gidan wata kwamishiniyar hukumar yaki da cin hanci a watan Fabrairun 2020 da ke unguwar Bassora ta nan Yamai ya yi sanadin mutuwar jami’in tsaron dake kare lafiyar wannan mata.

Saurari cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kai Hari Gidan Kakakin Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijar - 2'52"