Wasu sanannun 'yan siyasa daga yankin arewacin Najeriya sun yi taro a Abuja, inda suka kafa abinda suka kira Zauren maido da martabar siyasar yankin arewacin Najeriya.
Daya daga cikin jigogin wannan Zaure, Alhaji Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan Jihar Sokoto, ya fadawa wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu el-Hikaya cewa hadin kai yana da matukar muhimmanci ga mutanen arewa idan suna son maido da martabar siyasarsu, inda yace shekaru 15 da suka shige, yayi wannan magana cewa idan ba a yi haka ba, za a rika bi ana karkashe 'yan arewa har cikin gidajensu, kuma ga shi yanzu hakan na faruwa.
Yace 'yan arewa a kullum sai maganar Sardauna, abinda ya dace su yi shine kowa ya zamo Sardauna ta hanyar rungumar halayyansa domin a tafi baki daya, wanda Allah Ya ba girma a bi shi, maimakon hassada da zagon kasa.
Yace sauran sassan Najeriya kamar na Yarbawa da Igbo, duk kawunansu a hade yake, ban da na 'yan arewa.
Zauren, wanda ke karkashin jagorancin Tanko Yakasai, ya sha alwashin maido da martabar siyasar arewa ta hanyar kafa kwamitoci da sakatariyar da aka nada Dr. Umar Ardo a zaman sakatarenta.
Tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Dr. Bello Halliru, wanda ya bude taron da babban jawabi, yace a lokacin da aka tsaida Obasanjo yayi takara a 1999, ba mutanen yankinsa na Kudu maso yamma ne suka zabe shi ba, Arewa ce.
Yace a bayan da Obasanjo ya kare mulki aka maido da mukamin zuwa arewa, ba a kyale 'yan arewa suka zabi wanda suke son yayi musu takara ba, wasu ne suka tsayar da shi.
Yace makasudinsu a nan shine idan har an ce Arewa za a ba mulki, to a kyale su 'yan arewa su zabi wanda suke ganin zai yi ma kasa adalci su tsayar da shi.
Wadanda suyka halarci wannan taron sun hada da Paul Wampana, Nasiru Mantu, Buba Galadima, Ghali Na Abba, Babangida Aliyu, Idris Wada, Inna Chiroma, Zainab Maina da wasunsu.
Your browser doesn’t support HTML5