An Kafa Dokar Ta Baci Ta Tsawon Kwana 90 a Zambia

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu

Majalisar dokokin kasar Zambia ta kafa dokar ta baci a kasar ta tsawon kwana casa’in, bayanda shugaban kasar ya bayyana bukatar daukar wannan matakin makon jiya. Lamarin da mai yiwuwa ya kara ruruta rikicin siyasar kasar, masu sharhi kan lamura kuma suna cewa, yana iya kashe guiwar masu zuba jari da ake bukata a kasar dake dogara ga jan karfe.

Shugaban kasar ya yi kira da a kafa dokar ta baci ne bayanda wuta ta cinye babbar kasuwar dake babban birnin kasar wata guda da ya shige. Ya bayyana gobarar a matsayin wani hari da mutane marasa kishin kasa suka kai, a cikin jawabinsa ga kasa, ya bayyana cewa, wannan gobarar da kuma wadansu gobara da aka yi, wani abu ne da aka kitsa, wanda idan ba a dauki mataki ba, zai iya yin illa ga tattalin arzikin kasar, da kuma maida kasar baya.

Yan majalisar baki daya sun goyi bayan daukar wannan matakin jiya Talata. Babu dan jam’iyar hamayya ko daya da ya kada kuri’a domin an dakatar da 48 daga cikinsu a watan da ya gabata sabili da kin zama su saurari jawabin shugaba Edgar Lungu. Shugabansu Hakainde Hichilema yana kurkuku tun watan Afrilu inda yake fuskantar zargin cin amanar kasar. Yan majalisa kalilan da suka rage jiya sun kauracewa kada kuria.