An Kafa Wata Rundunar Tsaro Ta Musamman A Jihar Filato

Runduna Mai Yaki Da Haddasa Kashe-Kashe A Jihar Filato Da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kaddamar

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kaddamar da wata runduna ta musamman da za ta yi yaki da batagari da ke kashe-kashen rayuka da barnata dukiyoyin jama’a a jihar Filato.

PLATEAU, NIGERIA - Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun wanda ya kai ziyarar gani da ido kan asarar rayuka da dama a wasu kananan hukumomin jihar Filato, ya ce rundunar ta musamman da gwamnatin tarayya ta amince da kaddamarwa a jihohi goma na Najeriya, zata fara aiki ne nan take a jihar Filato.

Runduna Mai Yaki Da Haddasa Kashe-Kashe A Jihar Filato Da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kaddamar

Tuni da mataimakin Sufeta Janar na shiya ta hudu, Ebong Eyibio ya kaddamar da jami’an runduna ta musamman zuwa yankunan da ke fuskantar matsalolin tsaron.

A ci gaba da neman mafita kan batun kalubalen tsaron, Sanata mai wakiltar tsakiyar Filato, Diket Plang ya gabatar da wassu batutuwa a gaban majalisar dattawan, da ya ce za su taimaka wajen kawo dawwamammen zaman lafiya a jihar.

Runduna Mai Yaki Da Haddasa Kashe-Kashe A Jihar Filato Da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kaddamar

Sanata Diket Plang ya koka kan yadda maharan su dari hudu suka ratsa wurare suka mamaye kauyuka fiye da ishirin ba tare da wani ya gansu ba.

Ya kuma koka kan yadda wasu ke mamaye gonaki da gidajen wadanda suka yi gudun hijira, tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da jami’an tsaro na dindindin a yankunan.

Runduna Mai Yaki Da Haddasa Kashe-Kashe A Jihar Filato Da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kaddamar

A cewar Dah Mai’anguwa, Jamok Mafwalal Machambe daga gundumar Butura a karamar hukumar Bokkos, sun yi na’am da zuwan jam’an tsaron, ya kuma bukaci jama’a su basu goyon baya don samar da tsaro.

Sakataren kungiyar miyetti Allah a karamar hukumar Barkin Ladi, Abubakar Gambo yace suna bukatar jami’an tsaron su yi adalci.

Runduna Mai Yaki Da Haddasa Kashe-Kashe A Jihar Filato Da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kaddamar

Yayinda masu ruwa da tsakin ke kokarin lalubo hanyoyin samun mafita kan batun tsaron, tambayoyin da ke bakunan al’ummar Filato sune, su wanene ke aikata kashe-kashen, daga ina suke fitowa, me suke bukata, wanene ke ba su makamai da sauran kayan aiki, yaushe ne za su kammala aikin nasu? Lokaci zai bayyana abin da ke faruwa.

Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaddamar Da Wata Runduna Mai Yaki Da Haddasa Kashe-Kashe A Jihar Filato.mp3