A watan Nuwambar shekarar da ta gabata ne aka kafa shirin bunkasa al'ummomin kan iyaka a shiyar jihar Tahoua dake Nijar da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara dake cikin tarayyar Najeriya a karkashin inuwar hukumar hadin gwuiwar kasashen biyu tare da makasudin bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin al'ummomin kan iyaka.
Matakin farko na yarjejeniyar da gwamnonin jihohin hudu suka rabtaba wa hannu shi ne samar da hanyar sadarwa ta bai daya ga kafafen yada labarai a jihohin ta yadda za'a inganta fadakar da jama'a kan mahimmancin rungumar alamuran ci gaban al'ummominsu.
Wannan ne makasudin shirya taron shugabannin kafafen yada labarai kusan 47 a birnin Tahoua na jamhuriyar Nijar domin shata jadawalin aiki tare da fitowa da shawarwari na bai daya.
Gwamnan jihar Tahoua Musa Abdulrahaman shi ya kaddamar da bude taron ta wakilcin babban sakataren gwamnatin jihar Haruna Sakale. A cewarsa turawa ne suka shata iyakoki tsakanin al'ummominsu amma a akasarin gaskiya babu iyaka domin babu banbanci tsakanin 'yan Najeriya daga jihohin uku da mutanen Tahoua. Injishi dalili ke da yakamata su tashi daga barci kuma 'yan jarida ne zasu iya tada mutane daga barcin.
Wakilin gwamnan jihar Zamfara kuma mai bashi shawara ta musamman akan kula da lafiyar dabbobi Ibrahim Arzika Musa Maru ya ce sun zabi 'yan jarida ne domin idan aka yi tsari akwai inda ba'a iya zuwa amma labari zai kai walau ta hanyar rediyo, talibijan ko jaridu. Ta haka za'a aiwatar da abun da ake son mutane su fahimta dashi. Idan babu masu yada labarai da zasu kaishi inda ake bukata lamarin zai zama dirkaniya kawai.
Wakilin gwamnan Sokoto a taron kuma kwamishanan ciniki da yawon bude ido Bello Isa Ambarura yana ganin cewa kwaliya zata biya kudin sabulu duk da watsin da kwamnatin jihar ta yi na gina katafariyar kasuwar kasa da kasa a garin Illela.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5