Haka kuma ya kunshi fallasa abubuwan dake kama da yunkurin cin hanci ta yadda za a dauki matakin shara’a akan wadanda aka samu da aikata irin wadanan haramtattun dabi’u.
Reshen kungiyar Tournons la Page a Jamhuriyar Nijar ne ta hanyar ofishinta mai kula da tattara bayanai da ake kira Maison du Citoyen ya bullo da wannan sabon tsari dake hangen baiwa ‘yan kasar damar gabatar da korafe- korafe a duk lokacin da suka gano aikata aikin asha kamar yadda shugaban kungiyar Maikol Zodi ya bayana.
Kungiyar ta ce ta tanadi gogaggun masana doka masu alhakin bin diddigin kararrakin jama’a don kai irin wadannan maganganu a gaban kotu.
Rashin gabatar da rahotannin binciken zargin almundahana cin hanci da makamantansu a gaban shara’a ko jan kafar da ake fuskanta wajen daukan matakan hukunta wadanda aka kama da laifin aikata ba daidai ba, saboda dalilan siyasa na daga cikin matsalolin da kungiyoyin fararen hula ke korafi akansu a nan Nijer.
Hakan na faurwa ne yayin da mahukuntan kasar ke ikirarin cewa su na da kyakkyawar niyyar yaki da miyagun dabi’un dake yi wa tattalin arzikn kasa ta’annati.
Saurari cikakken rahaton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5