A yayin da masu ruwa da tsaki ke jaddada wajibcin gudanar da zabuka a dukkannin sassan Nijeriya, duk kuwa da fargabar da wasu ke nunawa game da yanayin tsaro a arewa maso gabashin Nijeriyar, wasu kungiyoyi masu zaman kansu da shugabannin addinai da sauran wadanda abin ya shafa sun hada kawunansu wajen jaddada muhimmancin gudanar da kampe da kuma zabuka cikin kwanciyar hankali.
Haka zalika, sun yi kiran da masu zabe su tabbatar cewa sun zabi shugabanni na gari da za su ciyar da kasar gaba. Wakilinmu a Abuja, wanda ya turo ma na da wannan rahoton, Nasiru Adamu Elhekaya ya ruwaito Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan na tabbatarwa cikin wani jawabinsa cewa babu makawa za a gudanar da zabuka a dukkannin wurare. Elhekaya ya kuma ruwaito mai bai wa Shugaban Shawara ta fuskar siyasa Alhaji Rufa’i Ahmed Alkali na cewa, bai kamata wasu su rinka cewa idan an zabi wani da ba su so duniya za ta tashi ba.
Ustaz Almakki Habibu wanda ya taho daga jihar Taraba na daga cikin wadanda su ka halarci taron, kuma y ace wannan karon hukumomin da abin ya shafa sun sami lokaci mai tsawo na shirye-shirye, don haka ya kamata su gudanar da zaben da kyau kuma lami lafiya. Ya ce rashin adalci ke sa mutane su ga kamar sai dan’uwansu ne kadai zai kare muradunsu na Kabila ko addini. Shi ma Alhaji Aliyu Ahmed Jamfalan, Sakataren Jama’atul Izalatul Bid’a wa’ika matus-Sunnah shiyyar Kaduna ya ce duk matsalolin Nijeriya na da nasaba da sakin hanyar imani zuwa ga sharholiyoyi da zunubai. Don haka, y ace kar a bi jam’iyya amma a zabi duk wani mutumin kirki ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ba.
Nasiru ya kuma ruwaito shugabannin Kirista ciki har da Oneyikan na kiran da a yi komai cikin natsuwa da tsaron Allah. Ya ce tuni su ka fara kokarin kawo kusanci tsakanin matasan mabiya addinan biyu. Ya ce har wasanni ma za a shirya tsakanin Musulmi da Kirista inda shugabannin addinan za su zama masu tsaron gida.
Your browser doesn’t support HTML5