An Ja Daga a Rikicin Shugabancin PDP

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido

Bayan da aka kammala taron gangami na babbar jam’iyar adawa ta PDP a birnin Fatakwal da ke jihar Rivers a Najeriya, har yanzu ana cigaba da takaddama kan waye shugaban jam’iyar a yanzu.

Shugaban jam’iyar da aka tsige Sanata Ali Modu Sherrif, da tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi da taron Fatakwal ya zaba a matsayin sabon shugaba, da kuma Sanata Nasiru Mantu da taron dattawan jam’iyar ya zaba a Abuja, kowanen sun a cewa shi ne shugaba jam’iyar.

Jam’iyar ta PDP ta shiga rudani ne tun bayan da ta fadi zabe a bara inda jam’iyar adawa a wancan lokacin ta APC ta karbe ragamar mulkin Najeriya bayan da ta kwashe shekaru 16 ta na mulki.

Yanzu haka manyan jam’iyar na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu dangane da wannan takaddama da ta kaure.

Saurari rahoton wakilin Muryar Amurka a Fatakwal, Lamido Abubakar Sokoto domin jin tsokacin da tsohon gwamnan jihar Jigawa da sauran mukarraban jam’iyar suka yi dangane da wannan cecekuce.

Your browser doesn’t support HTML5

An Ja Daga a Rikicin Shugabancin PDP - 3'10"