Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barazanar Korar Sanata Shehu Sani Da APC Tayi


APC
APC

Jam’iyyar APC shiyyar jihar Kaduna tayi barazanar korar Sanata Shehu Sani, a dalilin goyon bayan yajin aikin da kungiyar kwadago ke yi a Najeriya.

Jiya Alhamis ne sakataren yada labaran jam’iyyar APC shiyyar jihar Kaduna, Salisu Wusono, ya nuna rashin jin dadin jam’iyyar APC game da abin da Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya yayi.

Jam’iyyar APC dai na ganin goyon bayan kungiyar kwadago da Sanata Shehu Sani yayi, ya sabawa tsarin jam’iyyar dama shugaban Najeriya Mohammadu Buhari.

A nasa bangaren Sanata Shehu Sani, yace yana goyon bayan shugaba Mohammadu Buhari dari bisa dari, amma zai ci gaba da bayyana ra’yinsa akan duk muhimman batutuwan da suka shafi kasa.

Da yake mayar da martani kan barazanar, mai baiwa sanata shawara kan harkokin siyasa Suleiman Ahmed, yace Sanata na ganin wannan magana tamkar mafarki ce.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG