Zaben Ghana: An Harbe Wani Har Lahira

GHANA: Police logo

An riga an kai gawar mamacin dakin ajiyar gawarwaki domin adana da bincike, yayin da wanda ya jikkata ke samun kulawar likitoci.

Rundunar 'yan sandan Ghana ta tabbatar da kamen mutane 4 dake da hannu a harbin da aka yi a garin Nyankpala dake yankin arewacin kasar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda tare da jikkata wani.

An riga an kai gawar mamacin dakin ajiyar gawarwaki domin adana da bincike, yayin da wanda ya jikkata ke samun kulawar likitoci.

An kama wadanda ake zargi da hannu a harbin da aka bayyana sunayensu da Majid Issah da Fodi Issiage Kamara da Yakubu Sumaila da Alhaji Bashiru Muhammad da yammacin yau Asabar kuma a halin yanzu suna hannun 'yan sanda.

Hukumomi sun bayyana cewa mutanen suna taimakawa bincike a kokarin da ake yi na bankado musabbabin afkuwar mummunan labarin.

'Yan sanda sun jaddada aniyar tabbatar da adalci da tsaron al'umma, inda suka bukaci mazauna yankin su kwantar da hankulansu a yayin da ake cigaba da bincike.

Za a cigaba da samar da karin haske a kan lamarin da zarar an samu karin bayanai.