An fara kidayar kuri’u a rumfunan zabe bayan kammala kada kuri’a a fadin Ghana.
A mazabu da dama, jami’an zabe sun fara tattara sakamako, yayin da jama’a ke taruwa domin ganin yadda ake gudanar da kidayar cikin gaskiya da adalci.
Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan kasar ke dakon sanin wanda zai lashe manyan kujerun majalisar dokoki da ake takara, ciki har da shugabancin kasa.
An rufe kada kari'a da karfe 1700 GMT.
Yadda aka kirga kuri'u a wani rumfar zabe dake gundumar Ayawaso ta Gabas dake yankin Greater Accra
Dandalin Mu Tattauna