Sun kammala taron ne cikin dare Alhamis a birnin Accra, inda Muryar Amurka ta halarci daya daga cikin tarukan domin samun tattaunawa da wasu magoya baya.
A wurin taron jami’iyar NPP mai mulki, wasu ‘yan jami’iyyar sun bayyana wa Muryar Amurka kwarin gwiwar lashe zaben na ranar Asabar, 7 ga watan Disamba.
Yayin jawabinsa, ‘dan takarar jami’iyar na NPP mai Mulki kuma mataimakin shugaban kasa Dr. Mahmud Bawumia, ya ce jami’iyyarsu zata samu nasara, duba da irin ayyukan ci gaba da ta gudanar a cikin kasar da nasarori da ta samarwa kasar da kuma kyawawan manufofinta da take shirin aiwatar da su a sabuwar gwamnatinta.
Dr. Bawumia ya kara da cewa azahiri wannan zabe ne na zuwa kyakkyawar makoma ko kuma na komawa ga tsohon labari, abokin karawa na shine yake tsohon yayi, kuma wato shi Dr. Bawumia yake wakiltan makomar kasar.
Tuni kungiyoyin masu sa ido kan zaben suka shigo kasar domin tabbatar da ganin an gudar da zaben bisa gaskiya da adalci da kuma zaman lafiya.
Tsohon mataimakin Shugaban kasar Najeriya Mohammed Namadi Sambo dake jagorantar masu sa ido na ECOWAS ya yi kira da a gudanar da zaben cikin zaman lafiya.
Wakilai daga kungiyar Tarayyar Afirka ta AU suma sun isa kasar a jagorancin tsohon shugaban kasar Habasha Sahle-Work Zwede, haka zalika kungiyar Commonwealth ta kasashen renon Ingila ta turo wakilanta a jagorancin tsohon shugaban kasar Botswana Dr. Mokgweetsi Masisi.
Saurari cikakken rahoto daga Baba Yakubu Makeri:
Dandalin Mu Tattauna