An Haramtawa Dalibai Mata Saka Dan Mitsitsin Siket A Makarantun Jihar Anambra

Wasu dalibai a jihar Legas - Mun yi amfani da wannan hoto don nuna misali (Facebook/Lagos State)

Wannan sabon umarni da hukumomin jihar suka bayar na zuwa ne yayin da dalibai ke shirin komawa makaranta a ranar Litinin bayan kammala dogon hutu.

Hukumomi a jihar Anambra da ke kudu maso gabashi Najeriya sun haramtawa dalibai mata saka dan mitsitsin siket a makarantun jihar.

Kwamishinan Ilimi, Farfesa Ngozi Chuma, ce ta bayyana hakan, yayin wata ganawa da ta yi da sakatarorin ilimi daga makarantun gwamnati da na mishian a Awka, babban birnin jihar.

“Kwamishina na Allah wadai da yayin da ake yi na saka ‘yan kananan kayan makaranta, wannan ya sabawa ka’idojin saka kayan makarantun jihar.” Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’ar watsa labarai a ma’aikatar ilimin jihar, Obiageli Nwankwo ta ce.

Wannan sabon umarni da hukumomin jihar suka bayar na zuwa ne yayin da dalibai ke shirin komawa makaranta a ranar Litinin bayan kammala dogon hutu.

“Ka’idar saka kayan makaranta shi ne kada su gaza kai wa gwiwa, ba saman gwiwa ba kamar yadda ake yayi.

“Ya kamata mu cusawa dalibai kyakkyawar tarbiyar da ta dace, saboda su girma su zama mutane na gari.” Nwankwo ta ce.