Hakan ya bayyana ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan majalisar yankin Alhaji Abubakari Inusah, a madadin Ministan lafiya Stephen Yakubu, da aka tura wa manema labarai bayan wani taro na kwamitin ba da agajin gaggawa a fannin lafiyar al’ummar yankin da aka yi.
"An samu wasu mutane biyu da suka kamu da cutar a gundumar Binduri, inda daya daga cikinsu ya mutu. Bincike ya nuna cewa, sun ci wata dabba ne mai dauke da cutar anthrax," abin da Ibrahim Fusseini, jami’i a hukumar lafiya ta Ghana reshen gundumar Binduri ya fada wa Muryar Amurka kenan.
Ya kara da cewa, mutane 11 sun kamu da cutar ya zuwa yanzu, sannan dabbobi 4 sun mutu sanadiyyar cutar.
Majalisar ta umurci jami’an kula da dabbobi da su fara allurar riga kafin cutar ta anthrax nan take kuma an umurci masu dabbobi da su fito da dabbobinsu don a yi musu riga kafin cutar.
Wasu al’ummar yankin sun bayyana damuwarsu game da wannan kalubale da ya same su.
Malamin ilmin kimiya a makarantar sakandaren Bawku, ya ce, tun da cutar na kama dabbobi da mutane, suna rokon hukumar lafiya da ta yi kokari ta dakile cutar kafin ta kara yaduwa a cikin mutane da dabbobi.
Malami mai wa’azin addinin Musulunci a Bawku, Shaikh Musa Bagniya, a nasa bangaren ya yi kira ne da a gaggauta magance matsalar, kafin Sallar layya.
Namanga Mushiru, dan majalisar gundumar birnin Bawku, ya yi kira ga al’ummar yankin da su bi dokar da hukuma ta gindaya, tare da kai rahoton duk dabbar da ta mutu ga hukumar lafiya. Shi ma ya nanata kiran a yi kokarin magance matsalar kafin Sallar layya.
A nata bangaren ma'aikatar abinci da noma ta kasar, ta ce tana tabbatar wa jama'a cewa tana daukar dukkan matakan da suka dace don dakile cutar.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah Bako:
Your browser doesn’t support HTML5