Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Ba Da Izinin Amfani Da Maganin R21 Matrix


Maganin rigakafin zazzabin malariya
Maganin rigakafin zazzabin malariya

Gwamnatin Najeriya ta ba da izini na wucin gadi don amfani da maganin zazzabin cizon sauro na R21 Matrix, wanda masu binciken jami'ar Oxford suka kirkira.

Allurar rigakafi ce na cutar zazzabin cizon sauro ga yara masu shekaru watanni biyar zuwa watanni 36 kuma dole ne a adana allurar a yanayin zafi tsakanin digiri biyu zuwa takwas.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa, matsakaicin alkaluma na nuni da adadin sama da mutane 600,000 ne ke mutuwa a sanadiyyar zazzabin cizon sauro a kowace shekara, yayin da yaro daya ke mutuwa a duk minti daya.

Wadansu kananan yara dake jinyar zazzabin cizon sauro a asibiti
Wadansu kananan yara dake jinyar zazzabin cizon sauro a asibiti

Yara a Afirka ne suka fi fuskantar hadarin mutuwa daga wannan cuta. Sai dai kuma, masana kimiyya a jami'ar Oxford da ke Birtaniya sun ce sun shafe shekaru da dama suna bincike kan rigakafin.

Wannan ci gaban ya kawo sauyi a fagen yaki da zazzabin cizon sauro, wanda ke daya daga cikin manyan cutar dake kashe-kashen yara a Afirka.

Wani yana gwada maganin kashe zazzabin cizon sauro
Wani yana gwada maganin kashe zazzabin cizon sauro

An ce maganin yana da tasiri kashi 80% kuma Cibiyar Serum ta Indiya ta kera shi. Ghana ce kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta amince da fara amfini da rigakafin.

Hukumar Lafiya ta Duniya tana nazarin ko za ta amince da maganin, kuma ana shirin samar da allurai miliyan 200 a duk shekara.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG